بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
الفاتحة
Read Surah Al-Fatihah in Hausa (الفاتحة) with Arabic text, Hausa translation, and audio recitation. Chapter 1 of the Holy Quran, 7 verses — free online.
Quran in Hausa · all 114 Surahs
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;
ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
Mai rahama, Mai jin ƙai;
مَٰلِكِ يَوۡمِ ٱلدِّينِ
Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.
إِيَّاكَ نَعۡبُدُ وَإِيَّاكَ نَسۡتَعِينُ
Kai muke bautawa, kuma Kai kadai muke neman taimakonKa
ٱهۡدِنَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ
Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
صِرَٰطَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمۡتَ عَلَيۡهِمۡ غَيۡرِ ٱلۡمَغۡضُوبِ عَلَيۡهِمۡ وَلَا ٱلضَّآلِّينَ
Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.[1]
[1] Da cewa Ubangijin halittu ya tara ilmin tauhidi na Ilãhiyya da Rububiyya, Mai rahama Ya tãra dukan rahamar dũniya da rãyarwa da matarwa da ciyarwa da shãyarwa da tufãtarwa. Mai jin ƙai yã tãra ni'imar dũniya mai dõgewa zuwa Lãhira kamar ĩmãni da na lãhira. Mai mallaka ko Mai nũna mulkin rãnar sakamako, yã haɗa dukan wa'azi. Kai muke bautã wa kuma Kai muke neman taimako, ya tara tauhĩdin Ilãhiyya da ibãda amaliyya ko ƙauliyya. Hanya madaidaiciya, tã haɗa dukan sharĩ'a da hukunce-hukunce. Waɗanda aka yi wa ni'ima, yã tãra dukan tãrihin mutanen kirki. Waɗanda aka yi wa fushi, yã tãra dukkan tãrihin mãsu tsaurin kai. Ɓatattu, yã tãra tãrihin dukan mai aiki da jãhilci ko ɓata.
Al-Fatihah
Play